Yadda Zaki Hada Healthy Spanish.

Yadda Zaki Hada Healthy Spanish.

 

Healthy Spanish, girki ne da zakiyi wanda zaki iya yinsa kici a karin kumalon safe ki hadashi da shayi, kokuma kiyiwa yara don tafiya makaranta da safe. 


Abubuwan da zaki nema


  1. Albasa 1, 
  2. Dakalin Turawa 2,
  3. Kwai 3,
  4. Mai Cokali 3
  5. Sai gushiri yadda ya sauwaka. 


Yadda Zaki Hada. 


Dafarko ki samu albasarki mai kyau saiki yankata kanana-kanana, saiki samu wata yar tukunya saiki zuba. Ki kawo manki shima ki zuba akan Albasar, saiki bar-bada dan gishiri akai. Saiki juya sosai su juyu. Saiki dora a wuta yayi kamar mintuna biyar yadan dahu (Per Boil), saiki sauke a gefe. 


Saiki kawo dankalin turawanki ki yankashi kanana-kanana, saiki kawo wannan tunkunya da kikai per boiling din Albasarki ki zuba wannan dankalin turawan a ciki saiki da kuma sanya gishiri kadan karda yayi yawa tunda a wurin Albasar ma kinsaka saiki kuma dorawa a wuta yayi kamar mintuna 15 amma kuma kina dan juyawa duk muntuna biyar idan ya gama dahuwa saiki sauke. 
Zaki kawo kwanki saiki fasa ki kadashi sosai saiki zuba ruwan kwan naki a kan dafafen Dakalin Turawanki da Albasarki, ki juya sosai ya juyu.  Saiki kawo kaskoki na soya kwai saiki dora a wuta ki zuba mai saiki kawo wannan hadin saiki zuba a kaskon. Ki soyashi sosai kamar yadda kike soya kwai. 
masha Allah, Allah ya temaka kuma, don Allah ayi sharing zuwa WhatsApp Ko Facebook don yan uwa mata su amfana idan ke kinsani mutane dayawa irinki basu da wannan ilimin. 

 


Previous Post
Next Post

post written by:

0 Comments: