Muhimman Shawarwari Ga Maauratan Hausawa

Muhimman Shawarwari Ga Maauratan Hausawa

 


Yauwncin Ma'auratanmu na Hausawa kanyi tunanin aure abune kawai wanda sai basu damar saduwa ko samun yayaye, sukan mata da wasu wasanni wanda zaisa soyayya da kuma shakuwa su karu a tsakanin ma'aratan biyu. 


Wanda sauda dama idan Miji ko Mata ran daya ya baci basa sanin hanyoyin da zasubi su farantawa junansu rai, wanda zaisa wannan laifi ya fice a cikin zukatansu. 


Wadannan abubuwa kuwa sunada yawa amma mun tsakuro wasu zamuyi bayani a kansu. 


  • Yawancin ma'aurata yana da wuya kaga suna sumbatar juna a goshi koh a kumatu, kuma idan ka ga sun rungume juna, toh labari mai dadi ne ya samu.


Wannan dabi'a kuwa ta sumbata ko rugumar juna na daya daga cikin abu dake kara soyayya da shakuwa a tsakanin ma'arauta wanda in har basu subaci ko rugumar juna a wuniba yakansa miji ko mata suyita tunanin juna. 


Yake yaruwa ki daure ki koyi sumbata ko rungumar mai gidanki yayin farin cikin ku ko kuma bacin ransa, hakan zaisa ko laifi kikaimasa yayi saurin yafewa. 


  • Yakanyi wahala ka ga mata ko miji na baiwa daya abinci  a baki, hakan ka iya faruwa ne kawai idan daya babu lafiya. 


Wannan Al'ada ta bawa miji a binci a baki takanyi wuya a wurin macen bahaushe. 


Wanda wannna kuwa hanya ce babba da zaisa miji idan tafiya ta kamashi zuwa wani wuri zaici abin yake matukar tunawa da matarsa, kasancewar sabon da tayi masa na bashi a baki koda kuwa cokalin farko ne. 


  • Zabawa mai gida kaya da kuma dai-daita masa hular kansa, 


Mafiya yawan Matanmu na Hausawa kan zubawa mazajensu idanu yayin sanya kayan da zasu fita aiki ko kuma gyara musu hular kansu, 


Yake yar uwa tsayawa tsayin daka wajen zabawa mai gidanki kayan da zaisa dakuma dai-daita masa hular kansa, shima zaisa duk lokacin da wani abu yasameshi kamar zaiyi Alwala ya tube hularsa idan har zai maida ta ke zai fara tunawa a ransa yasan cewa dakina kusa dakece mai sata ki kuma gyarata. 


  • Yanada wuya kaga mu matan Hausawa munsayi kaya nasawa ko takalmi mun bawa mazajemu. 


Yawancimu bamu iya siyan kayan da mukaga yayi mana kyau, mu bawa mazajenmu su sanya. 


Yake yar uwa kisani cewa komai kudin mai gidanki idan kikasai kaya kika bashi yasanya a jikinsa to duk inda yaje kece zai dinga tunawa kuma ina alfahari dake akan wannan kaya da kika siya masa, wannan itama hnyace babba dazaisa mai gidanki ya jiki kullum kina zama sabuwa a wajensa.   • Yin Wanka da mai gidanki koda na tsarki ne. 


Sauda dama matar bahaushe takanji kunya tayi wanka tare da mai gidanta, 


Wanda yin wakan shima na daya daga cikin jigon shakuwa a tsakanin ma'aurata. 


Yanada kyau ki cire kunya ki ajiye a gefe kuna tafiya tare kuyishi tare da yan wassani na debe kewa, wanda ko a gurinne ya bukaceki yimaza ki buje masashi ya deba ladazaki samu.   • Rakiyar miji yayin fita wurin aiki. 


Yawancimu mukan zuba ido mu hausawa yayin fitar maigida zuwa aiki, kawai da zarar ya sallami mu ma'ana yabamu abubuwan da zamu yi amfani dashi na dafawa shikenan saimu manta rakashi a kofar gida ko bakin matarsa. 


Yake yar uwa kiyi kokarin koyar rakiyar mijinki zuwa bakin kofa ko kuma bakin matarsa kiyi kokarin bude masa kofar motar sannan kiyi masa hot kiss, zaiyi ta tunaninki har dawowarsa gida. Masha Allah muna fata yan uwa matanmu Hausawa zasuyi koyi da wadannna abubuwa da muka lissafa, dimin kuwa zai taimakeki sosai wajen sanun soyayya da shakuwa a wurin mai gidaanki kuma ko ina yaje kece abar tunaninsa a kowanne loakce. 


Don ALLAH  kiyi kokarin turawa yan uwa ta WhatsApp ko Facebook don suma su amfana da wannan shawar-wari. 

Previous Post
Next Post

post written by:

0 Comments: