Yadda Mata Zasu Gyara Fatar Jikinsu Tayi Hasake Da Tauahi

Yadda Mata Zasu Gyara Fatar Jikinsu Tayi Hasake Da Tauahi

 
Gyaran Jiki dai halak ne kuma ita tsafta na daya daga cikin cikon addini. 


Ita dai tsafta koda yaushe idan kina cikinta musan man ga matan aure tofa mai gida zaiji kullum na bukatar ya kasance dake a kusa dashi. 


Ga yan mata kuwa da zawarawa zaayi tayi musu layine a kofar gida na masoya masu kaunar su. 


Wannan dalili yasa muka binciko muku wannan surruka na gyaran jiki, wanda wannan hadi zai baki damar fatar jikinki tayi haske da kyalli sannan kuma fatar jikinki zatayi taushi sosai yadda zaki zama abin son mai gidanki ya shafa jikinki don laushi. 


Batare da bata lokaci ba sai kuyi maza ku nemi wadannan abubuwa kamar su:


  1. Kwaiduwar Kwai, 
  2. Kur-Kur, 
  3. Lalle, 
  4. Manja. 


Yadda Zaki hada wadannan kaya. 


Bayan "yaruwa ta tanadi wadannan kaya baki daya,  saita hadesu a wuri daya ta cakudasu sosai su juyu kibarsu suyi kamar mintuna goma bayan hadawa. Saiki dinga shafawa a jikinki yadda kike so, kodai ki shafa a Fuska da wuya kafafu da kuma hannaye. 


Kokuma ki shafe dukka jikinki baki daya bayan kamar yan mintuna 60 saikiyi wanka da ruwan dumi. 

Shike nan yaruwa insha Allahu zakiyi mamakin kyan da zakiyi cikin ya kwanki kalilan. 


Alhamdulllah muna fata zakuyi kokarin turawa yan uwa mata ta WhatsApp ko Facebook don suma su amfana da wannan magani Allah Yabada Sa'a na.

Previous Post
Next Post

post written by:

0 Comments: