Yadda zakiyi Gyaran Jikinki Donyin Kyau Da Kyalli.

Yadda zakiyi Gyaran Jikinki Donyin Kyau Da Kyalli.







Gyaran fata nada matukar muhimmanci a wajen duk wata ya mace domin kuwa mu mata anfi sanunmu da kyale-kyale. Sautari maza kanyi wanka kawai su shafa mai ne sufita harkokin gabansu amma kuwa mu mata mukankai mitinoni masu yawan gaske wajen yin kwaliya, 


Yar uwa kisani su mazajenmu sunfi son kullum suka taba fatar jikinmu sujita da laushi domin hakan kansa mai gida yawan rungumarki donyin wasa dake. 


Wannan dalili yasa muka kawo muku naganin da zaku gyara fatar jikinku tayi kyau tayi kyalli sannan tayi laushin gaske. 


A gurguje abubuwan da zaku nema sune. 


  1. Kur-Kur. 
  2. Lemon Tsami. 
  3. Bawon Kwai. 

Yadda zaki hadda maganin. 


Zaki daka kurkur naki sosai saiki kawo bawon kwai naki saiki daka shi, shima lemon tsaminki kuwa zaki iya shanyawa ya bushe saiki dakashi ki hadesu da ragowar da kika daka saiki dinga wanka dashi. Kokuma ki samu lemon tsamin ki matse ruwansa akansu saiki ki juya kiyi wankan dasu. 
Previous Post
Next Post

post written by:

0 Comments: